Isa ga babban shafi
Brazil-Amurka

Brazil zata bai wa Amurka damar kafa sansanin soji a kasar

Sabon shugaban Brazil Jair Bolsanaro, ya ce a shirye yake ya shiga tattaunawa da Amurka domin bai wa kasar damar kafa sansanin soji a kasar.Bolsanaro, ya shaida wa sakataren wajen Amurka Mike Pompeo cewa, yana fatan bude sabon babi don kyautata alaka a tsakanin kasashen biyu.

Jair Bolsonaro sabon Shugaban kasar Brazil
Jair Bolsonaro sabon Shugaban kasar Brazil CARL DE SOUZA / AFP
Talla

Sabon shugaban Brazil da aka rantsar a ranar talata, Jair Bolsonaro, jim kadan bayan kammala bikin rantsuwar ya sha alwashin yakar matsalolin cin hanci da rashawa da kuma na yawaitar kisan gilla da ‘yan kasar ke fama da su.

Bolsonaro mai ra’ayin rikau, ya sha alwashin aiki babu dare ba rana, wajen tabbatar da ci gaban Brazil.

Sabon shugaban, ya soma aiwatar da shirin sassauta dokokin mallakar bindiga a kasar, kamar yadda ya yi alkawari a baya, matakin da ya ce, zai taimakawa ‘yan kasar na gari wajen kare rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.