Isa ga babban shafi
Venezuela-Maduro

Maduro ya sha rantsuwar shugabancin Venezuela a sabon wa'adi

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro zai ci gaba da jan ragamar kasar a wani sabon wa’adin mulki bayan rantsar da shi a yau Alhamis, sai dai wa’adin na zuwa dai dai lokacin ya ke ci gaba da fuskantar suka daga kasashen duniya sakamakon tabarbarewar tattalin arziki mafi muni da kasar ke fuskanta baya yin karantsaye ga tsarin Dimukradiyya.

Maduro wanda tun bayan hawansa mulki tattalin arzikin kasar ke fuskantar koma baya babbar abokin dabinsa ta fuskar kasashe bai wuce Amurka ba, inda ko a yunkurin kisansa ya yi zargin da hannunta a ciki.
Maduro wanda tun bayan hawansa mulki tattalin arzikin kasar ke fuskantar koma baya babbar abokin dabinsa ta fuskar kasashe bai wuce Amurka ba, inda ko a yunkurin kisansa ya yi zargin da hannunta a ciki. REUTERS/Manaure Quintero
Talla

Rantsarwar wadda ke gudana a Kotun kolin kasar sabanin yadda aka yi tunanin cewa za ta gudana a gaban Majalisun wanda ke da rinjayen bangaren adawa, bata samu wakilci ko guda daya daga kasashe mambobin kungiyar EU ko na Lima ba.

Rahotanni sun nuna cewa kasashen Bolivia da Cuba da El Salvador da kuma Nicaragua da China da Turkiyya da kuma Rasha ne kadai suka tura wakilci don martaba bikin rantsar da shugaban don kama aiki.

Dai dai lokacin da Kotun kolin ta Venezuela ke rantsar Maduro a bangare guda hadakar kungiyar kasashen Latin Amurka na ci gaba da wani taron gaggawa a birnin Washington na Amurka don kalubalantar matakin sake shugabancin na Maduro a sabon wa’adi.

Shugaba Maduro mai shekaru 56 a watan Mayun bara ne aka kara zabensa duk da kauracewar galibin jam’iyyun adawar kasar sakamakon yadda ya ke ci gaba da rike da jagororinsu baya ga mayar da Majalisar zartaswar kasar ‘yar amshin shata haka zalika kotun Koli.

Shugaba Maduro wanda tsohon direban babbar mota ne kafin maye gurbin Hugo Chavez da ya mutu a karagar mulki, yanzu haka ya na da goyon bayan ilahirin sojin kasar haka zalika majalisu.

Haka zalika tun a bara, manyan kasashen duniya ciki har da Amurka da kungiyar tarayyar Turai ke ci gaba da caccakar nasarar ta Maduro inda suka bayyana zaben a matsayin mai cike da magudi da son rai.

Ko a makon jiya sai da kungiyoyin masu fafutukar kare Dimokradiyya suka mukaci Maduro ya yi murabus yayinda shi ma asusun bada lamuni na duniya IMF ya yi kiyasin cewa kasar za ta kara fadawa cikin matsalar tattalin arziki.

Tuni dai kasashen Latin Amurka suka bayyana cewa baza su ayyana Maduro a matsayin shugaba ba, batun da shugaban ke cewa zai dau matakin da ya kamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.