rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump Rasha Vladimir Putin

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya musanta boye bayanan ganawarsa da Putin

media
Shugaban Amurka Donald Trump da takwansa na Rasha Vladimir Putin bayan ganawa a garin Helsink. REUTERS/Leonhard Foeger

Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta zargin boye wasu muhimman batutuwa da ya tattauna akai da takwaransa na Rasha Vladmir Putin a shekarar 2017.


Trump ya musanta zargin ne a lokacin da yake mayar da martani ga Jaridar Washington Post, da ta rawaito cewa, ya kwace rubutun da tafinta yayi, bayan kammala ganawar tasa da Putin a garin Helsinki.

Zalika Rahoton na Washington Post, ya ce har yanzu babu wanda yasan inda aka boye tattaunawar tsawon awanni biyu da ta gudana tsakanin Trump da Putin a waccan lokacin, wadda aka nada.

Tun a shekarar 2016 dai, alaka tsakanin shugaba Trump da Rasha batu ne da hukumar binciken Amurka ta FBI ke nazari akai, bisa zargin tawagar yakin neman zabensa ta hada kai da jami'an Rasha, wajen taimaka masa  lashe zaben 2016, da kuma dakile farin jinin abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton.