rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Brazil

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Brazil ya sanya hannu kan dokar mallakar bindiga

media
Jair Bolsonaro sabon Shugaban kasar Brazil Reuters/路透社

Sabon Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya sanya hannu kan wata doka wadda zata saukaka yadda ake mallakar bindiga a cikin kasar, matakin da masu sa ido ke kallon cewar zai dada haifar da matsalar tsaro.


Shugaba Bolsonaro yace dokar zata baiwa yan kasa na gari damar mallakar bindiga domin kare kan su daga mahara.

Kasar Brazil ta gamu da kisan kai har sau 64,000 a shekarar 2017, abinda ya mayar da kasar daya daga cikin kasashen da suka fi hadarin zama a duniya.

Wata kididdigar bankin duniya ta ce, Brazil ce kasa ta 8 a duniya da aka fi kisan kai, yayin da, hukumomin tsaron kasar suka ce a shekarar 2017 an aikata kisan gilla dubu 63 da 883 a fadin kasar.

Shugaban kasar Jair Bolsonaro da tsohon kaftin din sojin Brazil mai ra’ayin rikau, Jair Bolsonaro ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a karshen makon watan Oktoba na shekara ta 2018, in da ya doke abokin takararsa Fernando Haddad da sama da kashi 55 na kuri’un da aka kada.