Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisa ta bukaci Trump ya jinkirta jawabinsa

Manyan kusoshin jam’iyyar Democrat a Majalisar Dokokin Amurka, sun bukaci shugaba Donald Trump ya jinkirta gabatar da jawabinsa dangane da halin da kasar ke ciki, lura da cewa har yanzu wasu ma’aikatun kasar na ci gaba da kasancewa a rufe.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Leah Millis
Talla

An dai tsara cewa shugaba Trump zai gabatar da jawabi dangane da halin da kasar ke ciki, da suka hada da batun tattalin arziki da dai sauransu a ranar 29 ga wannan wata na Janairu.

To sai dai kakakin majalisar wakilai wadda ‘yar jam’iyyar Democrat ce Nancy Pelosi, ta ce lura da yanayin tsaro da kuma kasantuwar wani bangare na ma’aikatun gwamnatin tarayya a rufe, akwai bukatar jinkirta gabatar da wannan jawabi.

Hukumar leken asiri da kuma ma’aikatar tsaron cikin gida, na daga cikin ma’iakatun da aka daina bai wa kudaden tafiyar da ayyukansu kimanin kwanaki 26 da suka gabata, abin da ke nufin cewa matsalar ta shafi hatta kare lafiyar shugaban.

Wannan ne karo na farko a tarihin Amurka, da aka dauki irin wannan dogon lokaci kusan kashi 25 na ma’aikatun kasar na rufe, sakamakon yadda Majalisar wakilai da ‘yan Democrat ke da rinjaye ta ki bai wa shugaban izinin ware Dala bilyan 5 da milyan700 domin gina katanga kan iyakar kasar da Mexico.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.