Isa ga babban shafi
Colombia

Yan bindiga sun kai harin makarantar yan Sanda a Bogota

Mahukunta a kasar Colombia sun ce mutane 21 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 68 suka samu raunuka a harin da aka kai wa makarantar horas da ‘yan sanda da ke birnin Bogota a jiya Alhamis.

Iván Duque Shugaban kasar Colombia
Iván Duque Shugaban kasar Colombia REUTERS/Luisa Gonzalez
Talla

Kawo yanzu dai ba wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, to sai dai ana danganta shi da fataken miyagun kwayoyi wadanda shugaban kasar ta Colombia Ivan Duke ya sanar da sanya kafar wando daya da su a lokacin da ya karbi ragamar mulkin kasar.

Colombia ta yi kaurin suna kan sha’anin miyagun kwayoyi musaman kungiyoyi dake ci gaba da taka rawa a wasu yankunan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.