Sanata Graham ya bukaci a hukunta yarima Salmane
Daya daga cikin manyan yan Majalisar dattawan Amurka, sanata Lindsey Graham ya bayana cewar Yarima Muhammad bin Salman na Saudi Arabia na da hannu wajen kashe dan Jarida Jamal Khashoggi, saboda haka ya zama wajibi a hukunta shi.
Wallafawa ranar:
Sanata Graham yace babu yadda za’ayi dangantaka tsakanin Amurka da Saudiya ta dore ba tare da hukunta Yarima Muhammad ba.
Dan Majalisa ya kuma bayyana shirin hukunta duk wadanda ake zargin suna da hannu wajen aikata kisan.
Tuni kasashen Amurka da Faransa da Canada suka sanya takunkumi kan mutane akalla 20 da ake zargin suna da hannu wajen aikata kisan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu