Isa ga babban shafi
Amurka-Trump

Jirage fiye da 600 sun fuskanci tsaikon sauka da tashi a Amurka

Matakin kulle ma’aikatun Amurka sakamakon kin amincewar Majalisar kasar wajen ware kudaden da za a gina Katanga tsakanin kasar da Mexico kamar yadda Donald Trump ya bukata ya fara shafar hatta al’amuran sufurin jiragen saman kasar.

Jinkirin dai ya shafi akalla jirage 137 da za su sauka a filin jirgin da kuma wasu 131 da ke shirin tashi daga birnin na Ney York wadanda suka fuskanci tsaiko na kusan sa’o’I 2 daga yadda aka tsara tun da farko.
Jinkirin dai ya shafi akalla jirage 137 da za su sauka a filin jirgin da kuma wasu 131 da ke shirin tashi daga birnin na Ney York wadanda suka fuskanci tsaiko na kusan sa’o’I 2 daga yadda aka tsara tun da farko. ©REUTERS/Michaela Rehle/File Photo
Talla

Hukumomin filin jirgin saman Guardia da ke birnin Newyork a kasar ta Amurka sun sanar da cewa jirage za su fuskanci tsaiko a tashi da ma sauka saboda karancin ma’aikata dalilin matakin gwamnati na gaza fitar da kudaden tafiyar da ma’aikatu.

Jinkirin dai ya shafi akalla jirage 137 da za su sauka a filin jirgin da kuma wasu 131 da ke shirin tashi daga birnin na Ney York wadanda suka fuskanci tsaiko na kusan sa’o’I 2 daga yadda aka tsara tun da farko.

Mai magana da yawun hukumar gudanarwar filin jirgin ya shaidawa manema labarai cewa tarin ma'aikatan filin jirgin yanzu haka na daukar hutu don laluben wani aiki na daban da za su samu kudaden kula da iyalansu, bayan matakin datse kudaden biyansu da Donald Trump ya yi.

Ka zalika akwai barazanar ci gaba da kulle wasu sassa na filayen jirgin saman kasar kuma kulle filayen dungurugum dai dai lokacin da ma'aikatun gwamnatin kasar ta Amurka ke shiga kwana na 35 ba tare da biyansu ko sisi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.