Isa ga babban shafi
Brazil

Fashewar dam ta shafi mutane dubu 24 a Brazil

Hukumomin Brazil sun bukaci kwashe akalla mutane dubu 24 daga muhallansu sakamakon fargabar sake fashewar wani dam na ruwa bayan wadda ta haddasa bacewar daruruwan jama’a baya ga asarar rayuka da aka samu.

Masu aikin agaji na ceton mutane da ibtila'in fashewar dam ta shafa a garin Brumadinho na Brazil.
Masu aikin agaji na ceton mutane da ibtila'in fashewar dam ta shafa a garin Brumadinho na Brazil. REUTERS/Adriano Machado
Talla

Akalla mutane 250 ne suka bace sakamakon fashewar dam din, ibtila’in da shi ne irinsa na biyu da ya fada wa kasar a kasa da shekaru hudu da suka gabata, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane kimanin 40.

Hukumar Kwana-Kwanan ta ce, ta ceto mutane 192 da ransu, yayin da 23 daga cikinsu ke kwance a asibiti saboda raunin da suka samu a ibtila’in wanda muninsa ya zarce makamancinsa na shekarar 2015.

Baya ga haddasa asarar rayuka, fashewar madatsar ruwar ta Samarco da ke garin Brumdinho, ta haifar da lakar da ta binne gaba daya wani kauye gami da gurbata ruwan kogi mafi girma a Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.