Isa ga babban shafi
VENEZUELA

Maduro ya yi watsi da bukatar Turai kan Venezuela

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ki amincewa da bukatar Kungiyar Kasashen Turai ta gudanar da wani sabon zaben shugaban kasa ko kuma kungiyar ta amince da jagoran 'yan adawa, Juan Guaido a matsayin shugaban kasa na riko.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro REUTERS/Manaure Quintero
Talla

Maduro ya ce, ba za su amince da duk wata tirsasawa daga Kungiyar Kasashen Turai ba, in da ya bayyana bukatar tasu a matsayin kuskure.

Kasashe irin su Spain ad Faransa da Birtaniya da Netherlands da kuma Jamus sun yi barazanar amincewa da Guaido a matsayin shugaba muddin Maduro yaki shirya sabon zabe.

A bangare guda, Amurka ta gargadi Venezuela cewa, za ta dandana kudarta muddin ta yi wa jami’an diflomasiyar Amurka ko kuma Guaido barazana.

Tuni Mr. Guaido da ke samun goyon bayan kasashen duniya, ya bukaci gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Maduro a ranar Laraba da Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.