Isa ga babban shafi
MASAR-FARANSA

Faransa za ta shirya taron addinai a Paris

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da ke kammala ziyarar kwanaki uku a Masar, ya bukaci gudanar da tattaunawa tsakanin addinai domin shawo kan matsalolin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa  da shugaba Abdel Fatah al-Sisi na Masar
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da shugaba Abdel Fatah al-Sisi na Masar AFP / Ludovic Marin
Talla

Shugaba Macron ya bukaci haka ne a ranar karshe ta ziyarar da ya kai Masar da nufin inganta dangantaka da kasar, yayin da ya bayyana damuwa game da take hakkokin bil’adama a kasar.

Macron da Fafaroma Tawadros na II sun jaddada bukataar gudanar da tattaunawa tsakanin addinai a yayin ganawarsu a babbar Majami’ar St. Mark da ta kasance shalkwatan kibdawa.

Macron da ya ziyarci wani karamin cocin da aka kai wa harin ta’addanci a shekarar 2016, ya ce, ya yanke shawarar shirya sabon taro da zai gudana nan da wani lokaci a birnin Paris game da wannan batu, koda yake bai yi cikakken bayani ba.

Wata majiyar diflomasiya ta ce, gwamnatin Faransa za ta karbi bakwancin taron tsirarun addinai a yankin Gabas ta Tsakiya, amma kawo yanzu babu rana ballanta wata.

A bagare guda, Macron ya gana da babban limamin Jami’ar Azhar, Sheik Ahmed al- Tayeb, in da suka tattauna kan horar da limamai a Faransa da kuma yaki da tsattsauriyar akida.

A yayin wannan ziyara dai, Macon da shugana Abdel Fatah al-Sisi sun cimma yarjeniyoyi har guda 30 na biliyoyin Euro da suka shafi bangarorin sufuri da ilimi da kuma lafiya, amma ban da makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.