Isa ga babban shafi
Venezuela

Shugaba Maduro ya shirya ganawa da yan Adawa

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro yace a shirye yake ya gana da yan adawar kasar dake samun goyan bayan Amurka da kuma gudanar da zaben ‘yan majalisu cikin kankanin lokaci.

Juan Guaido mai samun goyan bayan Amurka ,tareda  Nicolas Maduro wanda ke samun goyan baya daga Rasha
Juan Guaido mai samun goyan bayan Amurka ,tareda Nicolas Maduro wanda ke samun goyan baya daga Rasha REUTERS/Carlos Garcia Rawlins/ Miraflores Palace
Talla

Maduro dake hira da kamfanin dillancin labaran Rasha, yace a shirye yake ya zauna tare da ‘yan adawan saboda kare martabar Venezuela.

A daya geffen Kotun Kolin kasar Venezuela ta haramtawa Juan Guaido, mutumin da ya bayyana kan sa a matsayin shugaban riko izinin ficewa daga kasar, yayin da kuma ta rufe asusun ajiyar sa.

Shugaban kotun Maikel Moreno yace ya bada umurnin ne har sai lokacin da za’a kamala bincike kan zargin da ake masa na tinzira tashin hankali a cikin kasar.

Hukuncin kotun na zuwa ne bayan da ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace ta amince da shugaban majalisar a matsayin shugaban kasa na riko, kana kuma aka mika masa asusun ajiyar Venezuela dake Amurka.

Wannan mataki ya samu goyan bayan kasashen dake kudancin Amurka da Canada, yayin da kungiyar kasashen Turai da wasu kasashen dake yankin suka ce suma zasu amince da shugaban rikon muddin Maduro yaki kiran sabon zaben shugaban kasa.

Shugaba Maduro ya hau karagar mulki tun daga shekarar 2013 bayan rasuwar shugaba Hugo Chaves, sai dai zaben da akayi a watan Mayun bara ya gamu da suka daga kungiyar kasashen Turai da Amurka da kuma kungiyar kasashen Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.