rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Birtaniya Faransa Jamus Amurka Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Turai sun bullo da sabon tsarin ciniki da Iran

media
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi barazanar watsi da yarjejeniyar nukiliyar kasar muddin ba ta kawo musu wani alfanu ba AFP

Kasashen Jamus da Birtaniya da Faransa sun kirkiri wani sabon tsarin cinikayyar kasuwanci da Iran domin kauce wa takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasar.


Kasashen Turai sun dauki tsawon lokaci suna nazari kan wannan sabon tsarin kasuwancin da Iran wanda ya kunshi cinikayya tsakanin bangarorin biyu amma ba da takardun kudin Dala ba.

Koda yake akwai yiwuwar sabon tsarin ba zai fara aiki gadan-gadan ba har sai bayan wasu watanni sakamakon wasu bayanai da ake dakon su.

Manyan kasashen duniya da ke kawance da Amurka sun nuna adawarsu da matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na watsi da yarjejeniyar nukiliyar Iran wadda a sanadiyar ce aka dage wa kasar takunkuman karayar tattalin arziki.

Daga bisani Iran ta yi barazanar yanjewa daga wanann yarjejeniya har sai manyan kasashen Turai sun samar ma ta da kafar samun alfanun tattalin arziki, kuma tuni kasashen suka yi alkawarin tallafa wa kamfanoni wajen yin harkokin kasuwanci da Iran muddin kasar ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar.

Sabbin takunkuman Amurka dai, sun yi tasiri kan kamfanonin kasashen Turai ta hanyar tilasta musu jingine shirinsu na zuba jari a Iran.

dai gwamnatin Iran ta yi madalla da sabon tsarin cinikayyar, in da ta ce, mataki ne mai kyau.