rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Amurka Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta fice daga yarjejeniyar makaman da ke tsakaninta da Rasha

media
Tsohon shugaban kasar Amurka Ronald Reagan tare da tsohon shugaban Tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev a fadar Amurka ta White House yayin sanya hannu kan yarjejeniyar muggan makamai ranar 8 ga Disamban 1987 news.sky.com

Amurka ta bayyana shirinta na janyewa daga cikin yarjejeniyar da ta cimma da Rasha, ta haramta kera makamai masu linzami da ke cikin matsakaicin zango.Yayin sanar da matakin a yau Juma’a, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce matakin ya biyo bayan, saba ka’idojin takaita kera makaman masu linzami da Rashan ke yi.


Daga gobe Asabar, matakin na Amurka zai soma aiki, inda za ta soma aiwatar da shirin janyewa daga Yarjejeniyar baki daya, wanda za ta kammala cika sharuddan fita cikin wa’adin watanni 6.

Shugaba Donald Trump ya ce idan har Rasha na bukatar Amurka ta janye kudurinta na ficewa daga yarjejeniyar, tilas ne ta lalata baki dayan sabbin makamai masu linzamin da ta kera masu cin matsakaicin zango, hadi da sauran na’urorin harba su.

A shekarar 1987 shugaban Amurka Ronald Regan da takwaransa na tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev suka rattaba hannu kan yarjejeniyar wadda ta kunshi haramta kera nau'ikan makamai masu linzami, wadanda ke iya shafe nisan kilomita dari biyar zuwa dubu biyar idan aka harba su, zalika cikin matukar sauri da ya wuce mintuna suke isa wurin da suka nufa.

A gafe guda duk da cewa China ba ta cikin yarjejeniyar haramta kera makaman masu hadari, Amurka ta bayyana damuwa kan yadda kasar ke kara bunkasa ta fuskar karfin soja a nahiyar Asiya, inda ta ke ci gaba da kera makamai masu linzamin da ke cin matsakaicin zangon a yanayin da ya sabawa Yarjejeniyar ta 1987.