Isa ga babban shafi
Amurka- Venezuela

Amurka za ta yi amfani da karfin soji a Venezuela

Shugaba Donald Trump ya ce,  Amurka na iya amfani da karfin wajen shiga tsakani a rikicin siyasar Venezuela, yayin da kasashen yammacin Turai ke zafafa matsin lamba kan shugaba Nicolas Maduro don ganin ya sauka daga kujerarsa.

Shugaba Nicolas Maduro ya yi watsi da kiraye-kirayen kasashen yammacin duniya na ya sauka daga kujerarsa
Shugaba Nicolas Maduro ya yi watsi da kiraye-kirayen kasashen yammacin duniya na ya sauka daga kujerarsa REUTERS/Manaure Quintero
Talla

Shugaba Trump ya yi wannan bayanin ne a wata ganawa ta tashar talabijin, sai dai bai bada takamammiyar amsa ba ga tambayar da aka yi masa na ko me zai iya sanya kasarsa ta yi amfani da karfin soji a kasar da rikicin siyasa ya dabaibaye?

Trump ya ce, amfani da soji na iya kasancewa cikin zabin da kasarsa ke da shi game da rikicin siyasar Venezuela.

Tun a ranar 23 ga watan Janairu Amurka ta amince da jagoran ‘yan adawar Venezuela, Juan Guaido a matsayin shugaban kasa na wucen– gadi, yayin da take jagorantar wani gamgamin kasashe don ganin Maduro ya yi murabus.

Guaido ya hakikance cewa, tsarin mulkin kasar ya ba shi damar zama shugaba na wucen-gadi, duba da cewa zaben watan Mayun bara da ya ayyana Maduro a matsayin shugaban kasar haramtacce ne, wanda dole a yi watsi da shi saboda yadda aka hana manyan abokan hamayya takara.

A halin da ake ciki, wasu manyan kasashen Turai sun nuna alamun amincewa da  Guaido a matsayin shugaban rikon kwarya, in da suke cewa, gudanar da wani zabe shi ne mafita ga Maduro.

Da yake jawabi a wani taron magoya bayan gwamnatinsa don tunawa da zuwan Hugo Chavez a matsayin shugaban kasar shekaru 20 da suka wuce, Maduro ya yi watsi da kiran kasashen duniya na gudanar da wani zabe, maimakon haka, ya nanata batun zaben majalisar dokokin kasar ne kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.