rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Venezuela Faransa Jamus Sweden Spain Amurka Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Guaido ya samu goyon bayan kasashen Turai

media
Jagoran 'yan adawarVenezuela Juan Guaidó REUTERS/Carlos Garcia Rawlins

Kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da Sweden da Spain sun amince da jagoran ‘yan adawar Venezuela, Juan Guaido a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya. Wannan na zuwa ne bayan cikar wa’adin kwanaki 8 da suka bai wa shugaba Nicolas Maduro don ganin ya shirya gudanar da sabon zabe.


Firaministan Spain, Pedro Sanchez ya shaida wa manema labarai a birnin Madrid cewa, suna aiki tukuru don ganin an dawo da cikakken demokradiya a Venezuela ta hanyar mutunta ‘yancin bil’adama da kuma gudanar da zabuka baya ga kawo karshen garkame fursunonin siyasa a kasar.

Sanchez ya ce, ya amince da Juan Guaido a matsayin shugaban kasar Venezuela.

Shi ma shugaban Faransa, Emmanuel Macron a wani sakon Twitter da ya aika, ya ce, al’ummar Venezuela na da ‘yancin bayyana damuwarsu a demokradiyance, don haka, Faransa ta amince da Guaido a matsayin shugaban kasar na rikon kwarya domin aiwatar da shirye-shiryen gudanar da zabe.

Ita ma shugabar Gwamnatin Jamus, Angele Merkel cewa ta yi, za su ci gaba da tattaunawa da Guaido kan yadda zai fara shirye-shiryen gudanar da zabe nan ba da jimawa ba domin kuwa a yanzu, shi suke kallo a matsayin shugaban kasa na riko.

A yayin wani jawabi ta kafar talabiji, Firaministar Sweden, Margot Wallstrom ta ce, kuri’ar da ta kawo Maduro kan karagar mulki ba ingantacciya ba ce.

A can Birtaniya ma, Ministan Harkokin Wajen kasar, Jeremy Hunt cewa ya yi, sun bi sahun aminansu na kasashen Turai wajen amincewa da Guaido a matsayin shugaban Venezuela na wucen-gadi har sai an gudanar da sahihin zabe.

Tuni dai shugaba Maduro ya yi watsi da kiraye-kirayen kasashen na Turai na sake gudanar da wani zaben shugaban kasa a Venezuela, yayin da shugaba Donald Trump ya ce, akwai yiwuwar Amurka ta yi amfani da karfin soji wajen warware rikicin siyasar kasar.