Isa ga babban shafi
Kimiyar kiyo lafiya

An yi nasarar yin gwajin dashen goya koda A kan bera.

MASANA Kimiya sun bayyana samun gagarumar nasarar gwajin goya koda a jikin bera a wani yunkurin da zai bada damar yiwa Bil Adama dashen sa a shekaru masu zuwa.

Gwajin dashen goya koda ga bera
Gwajin dashen goya koda ga bera AFP
Talla

Yayin da masanan ke bayyana wannan gagarumar cigaba da aka samu a fannin lafiya, na fatan yi wa Bil Adama dashen kodar da aka goya a jikin bera nan gaba, sun kuma yi gargadin cewar wannan shine matakin farko na binciken, kuma akwai wasu matakai masu sarkakiya nan gaba da suka hada da yanayin aikin da kuma dokar kula da ayyukan da suka shafi kiwon lafiya wadda za’a shawo kan su kafin yiwa Dan Adam dashen.

Rahotan binciken da aka wallafa shi a mujallar kula da lafiyar da ake kira ‘Nature Communications’ yace sai an fara duba berar da ya dace ayi masa irin wannan dashe domin goya kodar, san nan ayi masa dashen kwayar halittar.

Bijnciken masana ya ce an samu gagarumar nasara wajen irin wannan gwaji da aka yi a jikin beran.

Farfesa Masumi Hirabayashi na Cibiyar Kimiyar Japan da ya jagoranci wannan bincike, ya kuma bayyana wasu shinge da ake bukata kafin ganin wannan aiki da suka sa a gaba ya samu nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.