Isa ga babban shafi
Dumamar yanayi-Duniya

Ana fuskantar yanayi mafi zafi a duniya

Wani rahoton masana yanayi ya nuna cewa, duniya na tunkarar yanayi mafi zafi fiye da wanda aka fuskanta shekaru 10 da suka gabata tun bayan fara bibiyar sauyawar yanayi a shekarar 1850.

Duniya na fuskantar barazanar yanayin zafi mafi tsanani
Duniya na fuskantar barazanar yanayin zafi mafi tsanani AFP PHOTO / LIONEL BONAVENTURE
Talla

Rahoton na zuwa a daidai lokacin da masanan ke ci gaba da gargadin illar da sauyawar yanayi za ta haifar ga halittun da ke doran-kasa.

Rahoton wanda masana yanayi suka fitar a ranar Laraba ya nuna cewa, kowacce shekara biyar mai zuwa nan gaba, zafin da ake fuskanta zai rika ninkawa kuma hakan na da nasaba da tururin da ma’aikatu ke fitarwa.

Tsananin zafin nan da shekaru biyar masu zuwa wanda zai kai digiri 1. 5 zai zamo mafarin zafin da duniya za ta fara fuskanta sanadiyyar sauyin yanayi matukar ba a dauki matakan da suka dace ba.

Rahoton ya ce, matukar hasashen na masana ya zo daidai da kididdigar da su ke yi a yanzu, zai zamo cewa, daga shekarar 2014 zuwa 2023, shi ne lokaci mafi zafi cikin shekaru 150 da suka gabata.

Ko a shekarar 2015, masana yanayin na duniya sun yi hasashen cewa, shekarar ita ce mafarin tsananin zafi da duniya za ta fara fuskanta.

Masanan sun ce, a kowacce shekara ana fuskantar yawaitar tsananin zafin kamar yadda suka yi hasashe a baya, matakin da su ke ci gaba da gargadin illar da rashin daukar matakan da suka dace ka iya haifarwa ga duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.