rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Turai ba ababen yarda bane - Khamenei

media
jagoran juyin juya halin musuluncin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei a Tehran June 12, 2009. REUTERS/Caren Firouz/File Photo

Jagoran addinin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce kasashen Turai ba ababen amincewa bane, duk da kokarin taimakawa Iran din da suke yi. Khamene’i ya furta kalaman ne yayin ganawa da manyan hafsoshin sojin saman kasar ta Iran.


Kalaman na Khamene’I na zuwa ne mako guda, bayan kaddamar da shirin kulla huldar cinikayya da Iran, da Birtaniya, Faransa da kuma Jamus suka yi, don dakile tasirin takunkuman karya tattalin arzikin da Amurka ta kakabawa kasar, bayan ficewarta daga cikin yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015 da suka cimma da kasar ta Iran.

Sabuwar huldar cinikkayyar da suka yi lakabi da INSTEX za ta baiwa Iran damar ci gaba da hulda da wasu kamfanonin kasashen nahiyar Turan, duk da takunkuman Amurka da suka haramta hakan.

Khamene’i ya kuma zargi kasashen Turai da munafunci dangane da batun kare hakkin dan adam, inda ya soki gwamnatin Faransa kan yadda jami’an tsaronta suka rika amfani da karfi kan masu sanye da rigunan dorawa da ke zanga-zanga, har ta kai ga tsiyayar da idanuwan wasu daga cikinsu.

Dangane da Amurka kuwa, jagoran addinin na Iran ya ce za su ci gaba da la’antar kasar da mummunan fata, muddin bata janye kudirinta a kansu ba, sai dai a cewar Khamene’i la’antar ta shafi shugaba Trump, sakataren harkokin wajensa Mike Pompeo ne da kuma mashawarcinsa kan tsaro John Bolton, banda sauran ‘yan kasar ta Amurka.