Isa ga babban shafi
EU

EU ta tona kasashen da suka gaza dakile halarta kudaden haramun

Kungiyar Kasashen Turai ta sanya jerin sunayen wasu kasashe da ake zargi da kasa dakile halarta kudaden haramun wadanda ake amfani da su wajen ayyukan ta’addanci da suka hada da Saudi Arabia da Najeriya da Panama.

Tutar kungiyar kasashen tarayyar Turai EU.
Tutar kungiyar kasashen tarayyar Turai EU. WTAQ.com
Talla

Daukar matakin ya haifar da suka mai karfi daga kasashen Turai da dama saboda yadda matakin kan iya shafar harkokin kasuwanci da kasashen da aka sanya sunayen su.

Bayyana sunayen wadannan kasashe 23 da ake zargi da kasa daukar kwararan matakai wajen dakile yadda mutane ke halarta kudaden haramun da kuma yadda ake amfani irin wadannan kudade wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci a duniya.

Kungiyar kasashen Turai tace wadannan kasashe na zama barazana ga zaman lafiya da kuma yaki da ta’addancin da ake samu.

Duk kokarin da akayi na ganin an fitar da sunan Saudi Arabia daga jerin kasashen yaci tura, saboda fargabar da ake da ita cewar matakin na iya sanya ta mayar da martanin wajen harkokin kasuwanci da kasashen dake cikin kungiyar Turai.

Jerin kasashen da ake yiwa irin wannan zargi ya kunshi Libya da Botswana da Ghana da Samoa da Bahamas da Bosnia Herzogovina da Guyana da Laos da Uganda da Vanuatu.

Sauran sun hada da Afghanistan da Koriya ta Arewa da habasha da Iran da Iraqi da Pakistan da Sri Lanka da Syria da Trinindad da Tobago da Tunisia da Yemen, sai kuma Nigeria da Panama da Saudi Arabia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.