rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sufuri

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Airbus zai daina kera jirgi mafi girma a duniya

media
Samfurin Airbus A380 Photo: Lionel Bonaventure/AFP

Kamfanin Airbus ya sanar da shirinsa na daina kera samfurin jirgin sama na A380 “Superjumbo” da ya kasance jirgin jigilar fasinjoji mafi girma a duniya.


A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kamfanin Airbus ya ce, nan da shekarar 2021 zai yi cinikin karshe na sayar da samfurin jiragen na A380 bayan ya shafe fiye da shekaru 10 a harkar kera-keran jirage.

Daukan matakin na zuwa ne bayan kamfanin jirgin fasinjoji na Emirates da ya kasance kwastaman da ke kan gaba wajen odar A380, ya rage yawan sayen jiragen.

Emirates mai shalkwata a Dubai ya rage odarsa daga jirage 162 zuwa 123 kamar yadda sanarwar ta bayyana a yau Alhamis.

Shugaban Airbus, Tom Enders ya ce, fasinjoji a sassan duniya na matukar kaunar zirga-zirga a jiragen na A380, yayin da yake cewa, matakin da suka dauka zai bakanta ran fasinjojin.

Kazalika masana tattalin arziki sun bayyana tsadar kudin sayan jiragen a matsayin daya daga cikin dalilan kawo karshen kera su.

A can baya dai, masanan sun gargadi cewa, akalla kamfanin na bukatar sayar da jiragen na A380 har guda 400 zuwa 600 kafin ya fara maido da uwar kudin da ya kashe wajen samar da su.