rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Tarayyar Turai Iran Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta gargadi kasashen Turai kan kawance da Iran

media
Pence ya ce lokaci ya yi da kawayen Amurka da ke Turai za su sake tunani wajen janyewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran REUTERS/Kacper Pempel

Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence ya bukaci kawayen kasar da ke nahiyar Turai da su janye daga cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran, inda ya ke cewa Amurka za ta sanyawa Iran karin takunkumi domin durkusar da ita.


Yayin da ya ke jawabi ga wani taron kasashe sama da 60 kan Gabas ta Tsakiya da ke gudana a kasar Poland da wasu manyan shugabannin kasashen Larabawa da kasar Isra'ila ke halarta, mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya bayyana Iran a matsayin babbar barazanar zaman lafiya da tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.

Pence ya kuma yi tir da wani sabon yunkurin da kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya ke yi na ganin kasashen Turai sun ci gaba da kasuwanci da Iran duk da takunkumin da Amurka ta sanyawa kasar.

Mataimakin shugaban Amurkan ya bayyana matakin a matsayin abin takaici wanda zai karfafa Iran da kuma raunata kasashen Turai ka na da raba Amurka da Turai.

Pence ya ce lokaci ya yi da kawayen Amurka da ke Turai za su sake tunani wajen janyewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran domin hada kai da su wajen cigaba da matsawa Iran lamba domin tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da duniya baki daya.