rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus Iran Amurka Isra'ila Syria Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen duniya 40 na taro kan tsaro a Munich

media
Ministan Harkokin Wajen Iran, Mohammad Javad Zarif na jawabi kan dandamali a zauren taron tsaro a birnin Munich na Jamus REUTERS/Andreas Gebert

An bude taron tsaron da ake gudanarwa a birnin Munich kowacce shekara wanda ya samu halartar shugabanni da ministocin tsaro da kuma hafsoshin soji daga kasashe akalla 40 na duniya.


Taron kashi na 55 na bai wa shugabanni da masana harkar tsaro damar nazari da tafka mahawara kan halin da ake ciki a duniya.

A yayin jawabi a zauren taron, Ministan Harkokin Wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya soki mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, yana mai bayyana wasu kalamai da Pence ya furta a matsayin nuna wariya da kuma jahilci.

Pence ya zargi Iran da kokarin kitsa sabon kisan kare dangi kan al’ummar Yahudawa.

Har ila yau, Zarif ya shaida wa taron cewa, bukatar da Pence ya gabatar wa kasashen Turai ta bin sahun Amurka wajen watsi da yarjejeniyar Nukiliyar Iran, tamkar yana shaida wa kasashen ne da su yi sakaci da sha'anin tsaronsu.

Kazalika Zarif ya zargi Isra’ila da takalar yaki saboda wasu hare-haren da ta kaddamar kan sansanonin sojin ta da ke cikin Syria.

A watan jiya Israila ta kaddamar da munanan hare-hare sama  kan sansanonin da ke dauke da sojojin Iran a Syria.