Isa ga babban shafi
Amurka

Jihohin Amurka 16 sun shigar da karar Donald Trump gaban Kotu

Wasu Jihohi 16 da ke Amurka sun maka shugaba Dobald Trump a gaban kotu saboda kaddamar da shirin dokar ta bacin da ya yi domin samar da kudin da zai gina Katangar da za ta killace iyakar kasar da Mexico, matakin da suka ce ya sabawa kundin tsarin mulki.

Ko a watan jiya, takaddama kan ware kudin ginin katangar tsakanim Trump da Majalisa ya haddasa kulle ma'aikatun kasar na kusan kwanaki 40
Ko a watan jiya, takaddama kan ware kudin ginin katangar tsakanim Trump da Majalisa ya haddasa kulle ma'aikatun kasar na kusan kwanaki 40 © Reuters
Talla

A ranar juma’ar da ta gabata, shugaba Trump ya bayyana dokar ta baci domin kaucewa bi ta majalisa wajen samun sama da Dala biliyan 5 da rabi da ya ke son yin amfani da su wajen gina Katanga.

Dokar da aka gabatar a kotun California ta ce shugaba Trump ya saba ka’ida domin majalisa ce ke da hurunmin amincewa da bukatar.

Jihohin da suka sanya hannu kan karar sun hada da California da Colarado da Connecticut ad Delaware da Hawaii da Illinois da kuma Maine.

Sauran sun hada da Maryland da Michigan da Minnesota da Nevada da New Jersey da New Mexico da New York da Oregon da kuma Virginia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.