Isa ga babban shafi
VENEZUELA

Mutane miliyan 3 sun tsere daga Venezuela

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, 'yan kasar Venezuela kusan miliyan 3 da rabi ne suka tsere daga kasar sakamakon rikicin siyasa da kuma karancin kayan more rayuwa da kasar ke fuskanta saboda tabarbarewar tattalin arziki.

Wasu daga cikin al'ummar Venezuela da ke cikin tsaka mai wuya
Wasu daga cikin al'ummar Venezuela da ke cikin tsaka mai wuya REUTERS/Edgard Garrido
Talla

Wata sanarwar hadin gwuiwa daga Hukumar Kula da 'Yan gudun Hijira ta Majalisar da Hukumar Kula da Kaurar Baki ta ce, kusan miliyan uku na wadanda suka bar kasar suka samu mafaka a kasashen makota cikin su har da Colombia da Peru, yayin da sauran kuma suka tafi kasashe da dama da ke kudancin Amurka.

Alkaluman hukumomin sun nuna cewar, a shekarar 2018 akalla mutane dubu 5 ke barin Venezuela a kowacce rana.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, muddin aka ci gaba da tafiya haka ba tare da daukar matakan da suka dace ba, tana hasashen cewar, mutanen da za su tsere daga Venezuela za su kai miliyan 5 da dubu 300 zuwa karshen wannan shekara.

Alkaluman hukumomin sun nuna cewar, kasar Colombia ta karbi 'yan Venezuela miliyan guda da dubu 100, sai Peru mai 506,000, sai Chile mai 288,000 sai Ecuador mai 221,000, Argentina mai 130,000 sai kuma Brazil mai 96,000.

Eduardo Stein, wakili na musamman na hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke Kula da Kaurar baki da kuma ta 'yan gudun hijira ya ce, kasashen da ke makotaka da Venezuela sun nuna dattako sosai wajen karbar bakin da kuma taimaka musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.