rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Australia Vatican

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta samu limamin coci da laifin lalata da yara

media
George Pell AAP Image/Erik Anderson/via Reuters

Wata Kotu a Australia ta samu wani babban limamin darikar Katolika kuma daya daga cikin masu bada shawara na kusa da Fafaroma Francis, George Pell da laifin cin zarafin wasu kananan yara biyu.


Masu taimakawa alkali yanke hukunci sun samu Pell da laifin lalata da kuma cin zarafin yaran biyu da ke Mujamiā€™ar St. Patrick a Melbourne a shekarar 1990.

Pell mai shekaru 77 shi ne mai rike da mukami mafi girma da aka taba samu da irin wannan laifi a gaban kotu.

Ana sa ran Me. Pell zai fara fuskantar hukunci daga ranar Laraba . Kodayake ya kaddamar da daukaka kara domin kalubalantar tuhumar da ake yi masa.