rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Korea ta Arewa Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump da Kim sun yi baran-baran a Hanoi

media
Donald Trump Kim Jong Un a birnin Hanoi na Vietnam REUTERS/Leah Millis

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nadama kan rashin cimma yarjejeniyar nukiliya da takwaransa na Korea ta Arewa, Kim Jong-Un, in da suka tashi baran-baran a ranar karshe ta ganawarsu ta birnin Hanoi


A yayin zantawa ta wayar tarho da shugaban Korea ta Kudu, Moon Jae-in, shugaba Trump ya ce, ya yi nadamar rashin cimma wata matsaya da Kim Jong-un na Korea ta Arewa bayan tattaunawar da ta gudana a tsakaninsu.

Sai dai wata sanarwa da fadar gwamnatin Korea ta Kudu ta fitar, ta ce, Trump din ya nuna aniyar warware batun na Korea ta Arewa ta hanyar sake shirya wata tattaunawa da kasar.

Kazalika Trump ya amince ya fara ganawa da Moon Jae-in kafin sake zama da Kim-Jong-un nan gaba.

A bangare guda, Trump ya ce, Mr. Kim ya bukace shi da ya sassauta takunkuman da aka kakaba Korea ta Arewa, bukatar da Trump ya ce, ba za ta yiwu ba.

Jim kadan da baran-baran din da suka yi a Hanoi, fadar gwamnatin Amurka White House ta ce, shugabannin biyu sun yi tattaunawa mai ma’ana kan kwance nukiliyar Korea ta Arewa da kuma bunkasa tattalin arzikinta. Sai dai kowanne ya kama gabansa a daidai lokacin da suke gab da daidaita huldar a tsakanin kasashensu.

Kodayake tun da farko, shugaba Trump ya yi watsi da hasashen cewa, tattaunawarsa da Kim za ta kai ga cimma wata yarjejeniya, yana mai cewa, ba zai yi gaggawar cimma matasya da Korea ta Arewa kan makamanta na nukiliyan ba.

A karo na biyu kenan cikin watanni takwas da shugabannin biyu ke ganawa da juna duk da cewa, a can baya sun yi musayar zafafan kalamai a tsakaninsu.