rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Rasha Zaben Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar dattijan Amurka ta fara bincike kan Donald Trump

media
Shugaban Amurka Donald Trump 路透社。

Kwamitin majalisar dattijan Amurka kan al’amuran Shari’a, ya kadamar da bincike kan zargin shugaban kasar Donald Trump, da aikata laifin hana Shari’a yin aikinta ta hanyar amfani da karfin kujerarsa ta shugaban kasa ba bisa ka’ida ba.


Shugaban kwamitin majalisar dattijan ta Amurka Jerrold Nadler ya ce sun soma binciken ne da tattara wasu shaidu, daga hukumomi, kungiyoyi da kuma mutane sama da 60.

Wasu daga cikin hukumomi da kuma mutanen da majalisar dattijan za ta nema domin tatsar bayanai daga garesu kan lamarin, sun hada da, ma’aikatar shari’ar Amurka, da ga shugaban kasar Trump Junior, da kuma Allen Wiesselberg, babban jami’i mai lura da hada-hadar kudaden kasuwancin shugaba Donald Trump.

Daya daga cikin zarge-zargen da Trump ke fuskanta daga ‘yan majalisun shi ne matakin tsige daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI James Comey cikin watan Mayun shekarar 2017, a dai dai lokacin da ya ke jagorantar wani binciken kwakwaf kan zargin hada baki tsakanin gwamnatin Rasha da Donald Trump, wajen taimaka misa lashe zaben 2016, sai kuma sauran sauye-sauyen mukaman muhimman ma’aikatu da hukumomin kasar da ake zargin Trump din ya yi da nufin dasa wadanda za su kare muradansa kadai.

Sai dai a martaninsa Trump ya ce ana son bincikar hada-hadar kudadensa ne, saboda rashin samun abin kamawa kan zargin da ake masa na bai wa Rasha damar yin tasiri a zaben Amurka.