rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Amurka Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Putin ya janye Rasha daga yarjejeniyar makamai ta INF

media
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Alexander NEMENOV / AFP

Shugaba Vladimir Putin na Rasha a hukumance ya sanar da janye kasar daga yarjejeniyar kera makamai ta INF wadda suka kulla da Amurka tun zamanin yakin cacar baka da ke da nufin hana kerawa da kuma bazuwar wasu nau’ikan makamai a duniya.


Cikin sanarwar da Fadar mulkin Rasha Kremlin ta fitar, ta ce Vladimir Putin ya sanya hannu kan sabuwar dokar da ke janye kasar daga yarjejeniyar makaman da aka kulla tsakanin Tarayyar Soviet da Amurka tun shekarar 1987, wadda ke da nufin haramta kera wasu nau’ikan makamai masu hadari.

Matakin na Rasha dai na matsayin martini ga Amurka wadda tun farko ta sanar da ficewa daga yarjejeniyar bayan da ta zargi Rashan da karya yarjejeniyar sakamakon kera wani nau’in makamin nukiliya mai cin dogon zango wanda ta ce na da hadari.

Shugaba Donald Trump na Amurka tun farkon shekarar nan ya tabbatar da ficewar Amurkan wadda ya ce za ta fita cikin watan Fabarairu yayinda za ta dauki tsawon wata 6 kafin kammala ficewar, yayinda Putin a nasa bangaren ya ce Rasha ma a shirye ta ke ta fice daga yarjejeniyar.

Tuni dai kungiyar tsaro ta NATO ta yi maraba da matakin Amurka tun a wancan lokaci, inda ta ce sabon makamin da Rasha ta kera mai cin dogon zango ta karkashin kasa ya saba sharuddan da kasashen biyu suka gindayawa yarjejeniyar, sai dai Majalisar Dinkin duniya ta yi gargadi kan illar da wargajewar yarjejeniyar za ta haifar ga tsaro.