rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Almundahana:Kasashen Turai sun kare Saudiya

media
Ministocin Kasashen Turai za su rattaba hannu a hukumance kan rashin amincewarsu da matakin sanya Saudiya cikin masu halasta kudaden haramun REUTERS/Francois Lenoir

Kasashen Turai sun yi watsi da bukatar da Hukumar Tarayyar Turai ta gabatar na sanya Saudiya cikin jerin kasashen da ke halasta kudaden haramun.


Wannan kudiri na Hukumar Turan ya fusata Saudiya da Amurka, yayinda ya yi mummunan tasiri kan kudaden shigar nahiyar Turai.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ta rawaito cewa, a ranar Alhamis ne Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Turai 28 za su rattaba hannu kan rashin amincewarsu da matakin a hukumance a wani taro da za su gudanar a birnin Brussels.

Ministocin sun ce, wannan shirin ba shi da alfanu ko kadan illa haddasa takun sakar diflomasiya da Saudiya.

Tuni Sarki Salman na Saudiya ya aike wa shugabannin Turai da rubutacciyar wasika, in da ya kalubalanci matakin.

Kasashen Iraqi da Pakistan da Habasha da Korea ta Arewa da Iran na cikin wadanda aka sanya cikin masu halasta kudaden haramun din.