Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Ana bikin ranar mata ta Duniya

Kowacce ranar 8 ga watan Maris, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar mata ta duniya domin karfafa gwiwar matan yin kafada-da-kafada tsakaninsu da takwarorinsu maza a fannonin rayuwa daban-daban.

MDD na son cimma daidaiton jinsin mata da maza a 2030.
MDD na son cimma daidaiton jinsin mata da maza a 2030. Feisal Omar/Reuters
Talla

Taken ranar matan a bana, ita ce ‘bunkasa tunani, hazaka samar da sauyi don daidaiton jinsi’, wanda ke da nufin wayar da kan jama’a a sassan duniya don shigar da mata kowanne bangaren rayuwa da nufin bunkasa ci gaba.

Matakin tsaida ranar a cewar Majalisar Dinkin Duniya bai wuce cimma muradin ganin an samar da cikakken daidaito tsakanin Jinsin maza da na mata ba, wanda ake da nufin cimmawa nan da shekarar 2030.

Karkashin kudirin ranar, akwai fatan ganin mata sun shiga kowanne fanni na rayuwa ba tare da barin ko da mace ko kuma yarinya 1 ba, kama daga matan karkara da kuma na birane, don samar da ci gaba mai dorewa, ba tare da nuna wariya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.