rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya Faransa Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An bude taron kare muhalli na duniya a Kenya

media
Emmanuel Macron lokacin taron One Planet Summit a birnin New York, 2018-09-26 REUTERS/Shannon Stapleton

Wakilan gwamnatoci, kamfanoni, cibiyoyin kudade da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, a wannan alhamis sun fara taro don tattauna batutuwan da suka shafi kare muhalli a birnin Nairobi na Kenya da ake kira One Planet Summit.


Wakilai sama da dubu hudu daga sassan duniya ne ke halartar taron, wanda ke cikin jerin tarurukan da Faransa ta bukaci a yi domin samar da kudaden da za a magance matsalar dumamar yanayi, bayan kulla yarjejeniyar duniya kan wannan batu a 2017 a birnin Paris.

Duk da cewa rawar da Afirka ke takawa wajen gurbata muhalli a duniya ba ta wuce 4% ba, to amma 65% na al’ummar nahiyar ne matsalar dumamar yanayin ta shafa, abin da masana ke cewa ya zama wajibi a dauki matakin taimaka wa nahiyar ta Afirka.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron za su gabatar da jawabai ga taron a wannan alhamis.