rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

New Zealand

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An yi Jana'izar wadanda suka mutu a harin Masallacin New Zealand

media
Wannan dai ne harin ta'addanci na farko da kasar ta New Zealand ta taba fuskanta a tarihi REUTERS/Jorge Silva

Yau an gudanar da jana’izar wasu daga cikin mutane da wani dan bindigar ya harbe a Masallatan juma’ar kasar makon jiya, yayin da Firaministar kasar Jacinda Ardern ta bukaci kasashen duniya su hada kai domin daukar mataki kan kafofin sadarwar da ke baiwa masu tsattsauran ra’ayi damar yada manufofin su.


Daruruwan mutane da suka hada da Musulmi da ma wadanda ba Musulmi ba ne suka halarci jana’izar a wata makabarta da ke kusa da Masallachin Linwood, daya daga cikin Masallatan da aka kai harin.

Firaminista Jacinda Ardern ta ce ya zama wajibi duniya ta dauki mataki kan kafofin sada zumunta.

A juma'ar da ta gabata ne dai, wani dan bidiga ya bude wuta kan mabiya addinin Islama da ke halartar sallar Juma'a tare da hallaka mutane 49.