Isa ga babban shafi
Iraqi

Mutane 100 sun mutu a hadarin jirgin ruwa a Iraqi

Adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin da wani jirgin ruwa ya yi a kogin Tigris da ke Mosul a kasar Iraki sun kai mutane dari, yayin da ake zaton adadin mamatan zai iya karuwa daidai lokacin da ake neman sauran mutanen da ke cikinsa.

Yanzu haka dai gawar mutane 71 aka iya tsamowa daga cikin ruwa yayinda ake ci gaba da lalube
Yanzu haka dai gawar mutane 71 aka iya tsamowa daga cikin ruwa yayinda ake ci gaba da lalube Arab.com
Talla

Ma’aikatar harkokin cikin gida a Iraqi ta tabbatar da mutuwar tarin jama’ar bayan nutsuwar kwale-kwalensu a Kogin Tgris na birnin Mosul lokacin da su ke kan hanyarsu ta zuwa yawon bude ido a daidai lokacin da ake bikin sabuwar shekarar Kurdawa.

Mai magana da yawun ma’aikatar cikin gidan ta Iraqi, Saad Maan ya ce jami’an agaji sun yi nasarar ceto mutane 55.

Wata majiyar tsaro ta ce cikin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin fiye da 70, har da kananan yara 19, inda Majiyar ta ce yanzu haka an kwashe tarin gawakin da aka gano a cikin kogin zuwa asibitocin birnin na Mosul.

Tuni dai Firaminista, Adel Abdel Mahdi ya umarci jami’an agaji su ci gaba da kai dauki don lalubo sauran muitanen da suka bace a hadarin kwale-kwalen, wanda bayanai ke cewa ya faru ne sanadiyyar daukar fasinjan da suka wuce kima.

Hadarin dai shi ne mafi muni da Iraqi ta fuskanta bayan makamancin cikin watan Maris din shekarar 2013 lokacin da wani kwale-kwale ya nutse a kogin Baghdad tare da hallaka mutane 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.