rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Donald Trump Isra'ila Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump zai ayyana Tuddan Golan a matsayin yankin Isra'ila

media
Shugaban Amurka Donald Trump Reuters/路透社

Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi ikirarin ayyana yankin Tuddan Golan da aka kwace daga hannun Syria a matsayin cikakken mallakin Isra’ila duk da rashin amincewar hakan daga kasashen duniya.


Cikin wani sako da ya wallafa a Twitter, Donald Trump ya ce bayan daukar tsawon shekaru 52 ana takaddama kan yankin na Tuddan Golan, lokaci ya yi da Amurka za ta mallakawa Isra’ila shi.

A cewar Trump la’akari da muhimmancin yankin ga tsaron Isra’ila da kuma zaman lafiyar duniya ya zama wajibi ya zamo karkashin ikon Isra’ila.

Wannan dai ne karo na biyu da Donald Trump ke yanke makamantan hukuncin bazatan da suka dau hankalin duniya, baya ga yunkurin sauya taswirar yankin gabas ta tsakiya.

Ko a shekarar 2017 ma, Donald Trump ya sha alwashin sauya matsugunin babban birnin Isra’ila daga Tel Aviv zuwa birnin Qudus, yankin da aka shafe shekaru ana takaddamar mallakarsa, wanda kuma daga bisani ya tabbatar da sauyawar.

Tuni dai Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi maraba da matakin na Amurka wanda ya ce matakin shi zai kawo karshen takaddamar tsawon shekaru 56, tun bayan kyakin kwanaki 6 da ya gudana a shekarar 1967.