Isa ga babban shafi
New Zealand

Mako daya da kai harin ta'addancin Christchurch

A wannan juma’a al’ummar kasar New Zealand sun zauna shiru na mintuna biyu domin tuna mutane 50 da wani dan ta’adda Brenton Tarrant ya kashe a masallatan juma’a makon jiya, yayin da aka rangada kiran sallah a fadin kasar wanda aka yada ta kafofin rediyo da talabijin.

Taron musulmi a masallacin Lakemba da ke Sydney don juyayin harin Christchurch, ranar 15 maris 2019.
Taron musulmi a masallacin Lakemba da ke Sydney don juyayin harin Christchurch, ranar 15 maris 2019. TAYYAB HAMEED/via REUTERS
Talla

Dubban mutane suka taru kusa da daya daga cikin masallatan da aka kai harin cikinsu har da Firaminista Jacinda Ardern, wadda ta bayyana cewar al’ummar kasar kamar gangar jiki ne, duk lokacin da wani sashe ya tabu, gaba-daya jikin zai kadu.

A daidai lokacin da ake kiran sallar da misalin karfe 1 da rabi na rana agogon New Zealand, mutane a kasar Australia ma sun tsaya cik a tituna domin nuna alhini ga wadanda aka kashe.

An bayyana dan ta’addar da cewa dan asalin kasar ta Australia ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.