rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Syria Isra'ila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ya kamata Amurka ta yarda Golan mallakin Isra'ila ne-Trump

media
Tsaunukan Golan, da Isra'ila ta mamaye tun 1967. REUTERS/Ammar Awad

Syria ta yi kakkausar suka ga matakin da shugaba Donald Trump ya dauka, da ke cewa ya kamata Amurka ta goyi bayan Isra’ila ta mayar da Tuddan Golan na Syria a matsayin mallakin Isra’ilan.


Sanawar da gwamnatin Syria ta fitar, ta bayyana matakin a matsayin wanda ke bayyana zahirin Amurka na kasar da ke kin mutunta dokokin duniya.

Tuddan Golan dai mallakin Syria ne da Isra’ila ta mamaye lokacin yakin kwanaki 6 da aka fafata tsakanin Isra’ilan da kuma kasashen Larabawa a 1967, to sai dai ba wata kasar duniya ta yarda cewa yankin mallakin Isra’ila ne sai a wannan lokaci na mulkin Donald Trump.

Trump ya sanar da wannan mataki ne daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ke ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya, ziyarar da Amurka ta ce Pompeo na yi domin kawo karshen tasirin Iran a yankin.

A shekara ta 2017 ma dai shugaban na Amurka ya yi wa duniya ba zata, inda ya bayyana birnin Quds a matsayin fadar gwamnatin Isra’ila, duk da cewa birnin na karkashin kulawar dokokin duniya ne.