rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

New Zealand Turkiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Erdogan ya bukaci yaki da kyamar Musulmi a duniya

media
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan Adem ALTAN / AFP

Shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan ya bukaci kasashen duniya da su yaki akidar kyamar Musulmi kamar yadda suka tashi tsaye wajen yakar akidar kyamar Yahudawa bayan kisan kare dangin da aka yi wa Yahudawan.


Kiran Erdogan na zuwa mako guda da harin da wani dan rajin fifita farar fata ya kaddamar kan al’ummar Musulmai a wasu Masallatai biyu da ke birnin Christchurch na New Zealand, in da ya kashe mutane 50 da suka hada da kananan yara da mata.

Gwamnatin New Zealand ta jaddada wa Musulmai cewa, za su ci gaba da rayuwa a cikin kasar ba tare da wata fargabar tsaro ba.

Al'ummar kasar sun nuna goyon bayansu ga Musulman bayan wannan kazamin harin da Firaministar kasar, Jacinda Ardern ta bayyana  a matsayin na ta'addanci.