Isa ga babban shafi
Turai - China

Kasashen Turai sun gana da China kan kyautata alakar Kasuwanci

Shugabannin kasashen Turai sun bukaci kyautata alakar cinikayya da tattalin arziki tsakaninsu da China, wadda za ta amfani kowane bangare, ba tare da nuna son zuciya ba.

Shugaban majalisar kungiyar EU Jean-Claude Juncker, shugaban Faransa Emmanuel Macron,  shugabar Jamus Angela Merkel tare da takwaransu na China Xi Jinping a birnin Paris. 26/3/2019.
Shugaban majalisar kungiyar EU Jean-Claude Juncker, shugaban Faransa Emmanuel Macron, shugabar Jamus Angela Merkel tare da takwaransu na China Xi Jinping a birnin Paris. 26/3/2019. AFP / ludovic MARIN
Talla

Shugabannin na EU, sun jaddada bukatar ce yayin ganawa da tsakaninsu da shugaban China Xi Jingpin da ya ziyarci birnin Paris.

Yayin ganawa da shugabannin Faransa da Jamus, wato Emmanuel Macron da Angela Merkel da kuma shugaban majalisar kungiyar EU Jean Claude Juncker, shugaban China Xi Jinping yayi kokarin sauya tunanin jagororin na Turai dangane da damuwarsu kan karfin da China ke kara samu a kasuwannin nahiyar.

Yayin taron kungiyar tarayyar Turai ta kuma bukaci China ta cika alkawarin hada giwa da ita wajen aiwatar da manyan ayyukan shimfida titunan Jiragen kasa da na mota daga nahiyar Asiya zuwa ta Turan.

A farkon watan da muke ciki kungiyar kasashen Turai EU ta wallafa wani rahoto da ke bayyana China a matsayin babbar abokoiyar hamayyarsu a fannin kasuwanci, gabannin taron da zai gudana tsakanin bangarorin 2 a ranar 9 ga watan Afrilu.

Kasashen nahiyar Turai da China dai tare suke fuskantar kalubalen shawo kan barazanar fifita Amurka da shugaba Donald Trump ke aiwatarwa, ta fuskokin alakar kasuwanci inda ya kakabawa kayayyakinsu karin haraji, sai kuma ta fuskar Dilomasiyya da har yanzu kasashen Turan da China ke takkadama da Amurka kan batun Yarjejeniyar Nukiliyar Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.