rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Japan Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An sake tsare tsohon shugaban Nissan a Japan

media
Carlos Ghosn Tsohon Shugaban kamfanin Nissan Reuters

Hukumomin kasar Japan sun sake kama tsohon shugaban kamfanin hada motocin Nissan, Carlos Ghosn kan wasu zarge zargen amfani da kudade ta hanyoyin da basu kamata ba.


Jamiā€™an tsaron jiya alhamis sun yi sammako zuwa gidan Ghosn dake Tokyo inda suka tsare shi kan abinda suka kira kwashe kudaden ajiyar kamfanin Dala miliyan 15 wanda suka ce Ghosn yayi amfani da Dala miliyan 5 daga cikin su.

Ghosn ta hannu wakilin sa yayi watsi da zargin inda yake cewa ba zai karya masa gwuiwa ba.

A zaman kotun na baya tsohon shugaban Kamfanin kera motoci na Nissan, Carlos Ghosn ya shaida wa wata kotu a birnin Tokyo na Japan cewa, an yi kuskuren zargin sa da kuma tsare shi kan badakalar cin hanci da rashawa a kamfanin.