An samu raguwar yanke hukuncin kisa a Duniya- Amnesty
Wani rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty ya ce aiwatar da hukuncin kisa a fadin duniya ya ragu ainun, fiye da yadda lamarin ya ke a shekaru goma da suka wuce, yayin da a wasu daidaikun kasashe an samu karuwar irin wannan hukunci da kuma aiwatar da shi.
Wallafawa ranar:
Rahoton da kungiyar kare hakkin bil adama na Amnesty ta fitar a ranar Laraba na nuni da cewa, batun aiwatar da hukuncin kisa a Iran ya ragu matuka da kashi 50 cikin dari, biyo bayan sauye sauyen da ta gudanar a dokokinta kan muggan kwayoyi, haka ma lamarin ya ke a Iraqi, Pakistan da Somalia.
Rahoton ya ci gaba da cewa hukuncin kisa, tare da aiwatar da shi ya karu a kasashen Belarus, Japan, Singapore da Sudan ta kudu da Amurka, yayin da Thailand ta dawo da aiwatar da hukuncin a karon farko cikin shekaru goma, sai kuma Sirilanka da ke barazanar bin sahun Thailand.
An samu ci gaba kamar yadda rahoton ya nuna, inda jimilla, yawan hukuncin kisa ya fadi a fadin duniya, daga 993 a shekarar 2017, zuwa akalla 690 a shekarar da ta gabata.
Wannan alkaluma da kungiyar ta Amnesty ta fitar babu ta China a ciki, wacce duk duniya babu kasar da ta kai ta aiwatar da hukuncin kisa, inda ake boye adadin a matsayin wani babban sirri na kasa, kungiyar ta kiyasta cewa dubban mutane ne ake yanke wa hukuncin kisa kuma ake aiwatar da shi duk shekara a China.
Wannan nazari na shekara shekara da kungiyar ta Amnesty ta yi dai ya nuna cewa kokarin da ake na hana yanke hukuncin kisa da aiwatar da shi a duniya ya na samun goyon baya, duba da yadda wasu kasashe suka bi sawun masu soke hukuncin kisa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu