Isa ga babban shafi
Turai

Suka daga kasashe bayan cafke Julian Asange

Shugaban kasar Bolivia Evo Morales, ya yi kakkausar suka kan kutsen da ‘yan sandan Birtaniya suka yi cikin ofishin jakadancin kasar Ecuador da ke London don cafke mamallakin shafin fallasa bayanan sirri na Wikileaks wato Julian Assange a jiya alhamis.

Julian Assange, jagoran shafin  Wikileaks yan lokuta bayan cafke a ofishin jakadancin Ecuado
Julian Assange, jagoran shafin Wikileaks yan lokuta bayan cafke a ofishin jakadancin Ecuado REUTERS/Henry Nicholls
Talla

‘Yan sandan Ingila sun ce sun kama Assange wanda ya share kusan shekaru 7 yana samun mafaka a ginin jakadancin saboda ya saba wa sharuddan da aka gindaya masa.

Assange, mai shekaru 48 da haihuwa, ya sami mafakar siyasa a ofishin jakadancin kasar ta Ecuador da ke birnin London, tun a ranar 19 ga watan Yuni shekarar 2012, don kaucewa mika shi kasar Sweden, inda ake zargin shi da laifin yin fyade.

Assange yace ya na fargabar idan aka mika shi Sweden, daga can kuma za a iya mika shi Amurka, don a tuhume shi da laifin leken asiri.
Assange wanda dan asalin kasar Australia ne, ya share tsawon shekaru 7 boye a ofishin jakadancin kasar ta Ecuador .

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.