Isa ga babban shafi
Faransa

"Faransa ce ke sayar wa Saudiya da makaman yaki a Yemen"

Wasu bayanan sirri da aka bankado sun nuna cewa, Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudi Arabiya na amfani da makaman da suka saya daga Faransa wajen kai hare-hare a Yemen.

Mutane kimanin dubu 10 sun rasa rayukansu a yakin Yemen
Mutane kimanin dubu 10 sun rasa rayukansu a yakin Yemen IRNA
Talla

Bayanan sirrin sojin Faransa da aka wallafa a kafafen yada labarai, sun nuna cewa, Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudi Arabiya sun girke makaman da suka saye daga Faransa da suka hada da atilari da jiragen ruwa a yakin da suke gwabzawa da mayakan Huthi na Yemen.

Sai dai gwamnatin Faransa da ke shan matsin lamba daga Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama, ta hakikance cewa, kasashen na amfani da makaman ne wajen kare kansu daga hare-haren mayakan Huthi, amma ba wajen kashe su ba.

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adaman na zargin Faransa da hannu wajen aikata laifukan yaki a Yemen, in da kimanin mutane dubu 10 suka rasa rayukansu, baya ga miliyoyi da ke fama da barazar yunwa.

Faransa wadda ita ce ta uku wajen sayar da makamai ga kasashen duniya, na kallon Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin aminanta da ke yi mata biyayya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ana ganin wannan ne ya sa Faransar ta yi watsi da kiraye-kirayen dakatar da sayar da makamanta ga kasashen biyu, ba kamar Jamus ba da tuni ta daina sayar musu da makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.