Isa ga babban shafi
Faransa

An kashe gobarar Cocin Notre Dame a Faransa

Da misalin karfe 3 na daren da ya gabata ne jami’an kwana-kwana suka yi nasarar kashe gobarar da ta tashi a Mujam’ar Notre Dame da ke birnin Paris a kasar Faransa, daya daga cikin wuraren ibaba mafi dadewa a duniya.

Mujami'ar Notre Dame bayan kashe gobarar da ta tashi a cikinta.
Mujami'ar Notre Dame bayan kashe gobarar da ta tashi a cikinta. REUTERS
Talla

Mujami’ar wadda aka gina kusan shekaru 900 da suka gabata, ta kasance wuri mafi daukar hankalin maziyarta a yankin Turai baki daya, in da ake samun baki kimanin miliyan 13 da ke ziyartar Cocin a kowaacce shekara.

Faruwar wannan lamari ya yi sanadiyar dakatar da jawabin da ya kamata shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya gabatar a yammacin ranar Litinin, in da ya jagoranci tawagar jami’an gwamnatinsa domin kai ziyara a wurin da gobarar ta auku.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Macron ya ce, "wannan mujami’a, za mu sake gina ta, domin kuwa cibiya ce da ke alamta kasar Faransa, tun daga wannan Talata, zan bayar da umurnin fara wannan aiki"

"Idan ta kama za mu nemi kwararru hatta daga kasashen ketare domin sake gina wannan mujami’a." in ji Macron.

Yanzu haka  ana ci gaba da aikewa da sakonnin nuna damuwa dangane da faruwar wannan lamari, kuma daga cikin wadanda suka aike da irin wannan sako har da shugaban Amurka Donald Trump, da babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker.

Har ila yau an samu irin wadannan sakonni daga gwamnatocin kasashen Turai da Masar da kuma Iran, sai kuma fadar Vatican da ta Anglican da tsohon shugaban Amurka Barrack Obama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.