Isa ga babban shafi
Amurka- Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta bai wa Amurka sharadi kan nukiliyarta

Kasar Korea ta Arewa ta bukaci Amurka ta cire Sakataren Harkokin Wajenta, Mike Pompeo daga tattaunawar da su ke dangane da bukatar Amurkar ta ganin ta lalata makamanta na nukiliya.

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jon-un
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jon-un KCNA via REUTERS
Talla

Kiran na Korea ta Arewa na zuwa sa’o’i kalilan bayan ikirarinta na gwajin wani makami mai linzami a ranar Alhamis.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Korean ta fitar ta bayyana Mike Pompeo a matsayin mai sakaci kuma marar kwarewa.

Darakta Janar na ma’aikatar da ke Kula da Huldar Korea ta Arewa da Amurka, Kwon Jong Gun, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na KCNA cewa, matukar Pompeo ya sake shiga tattaunawarsu da Amurka nan gaba, babu shakka ganawar ba za ta yi armashi ba.

Jong Gun ya ce, shugaba Kim Jong Un na ganin dole ne Amurka ta sauya wasu tsare-tsarenta matukar ta na bukatar dorewar tattaunawar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Mike Pompeo ke fuskantar caccaka daga Korea ta Arewan ba, tun bayan fara kyautata alaka tsakanin kasar da Amurka cikin watan Yunin bara.

Tun bayan tashi baram-baram a ganawar Vietnam a farkon shekarar nan, Pyongyang da Washington suka fara takun-saka, ko dai shugaba Kim ya ce, a shirye yake su kara wata tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.