Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Amurka za ta dauki mataki kan masu cinikayya da Iran

Amurka ta gargadi kasashen da ke sayen man fetur daga Iran a nahiyar Asiya da su gaggauta kawo karshen cinikayyar da ke tsakaninsu ko kuma su fuskanci takunkumanta. Matakin na Amurka sabon yunkuri ne na ganin ta kara matsa lamba ga Iran wadda ke fuskantar takunkuman karayar tattalin arziki.

Daya daga cikin cibiyoyin mai na Iran
Daya daga cikin cibiyoyin mai na Iran REUTERS/Raheb Homavandi/File Photo
Talla

Matakin Amurkan na zuwa a dai dai lokacin da aka fuskanci hauhawar farashin man a kasuwannin duniya da akalla kashi 3, tashin farashi mafi kololuwa a cikin shekarar nan.

Sai dai wata majiya ta shaida wa Jaridar Washington Post cewa, kai tsaye wasu kasashen na Asiya za su kalubalanci sabon matakin na Amurka.

Kasashen da Amurkan ke gargadi har da India wadda ke matsayin babbar abokiyar cinikayyar man fetur ga Iran, da Iraqi wadda ko a baya-bayan nan Amurkan ta sake yi mata gargadi kan yadda bangaren manta ya dogara da Iran.

Yanzu haka, farashin man Fetur a kasuwannin duniya ya kai Dala 74 da Centi 31 kan kowacce ganga bayan tashi da akalla kashi 3, wanda kuma shi ne karon farko tun bayan watan Oktoban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.