Isa ga babban shafi
Srilanka

Kasashen duniya sun hada baki wajen yin tir da Harin Sri Lanka

Shugabannin kasashen duniya sun hada kai wajen yin tir da jerin hare haren ta’addancin da aka kai Sri Lanka wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 200, cikin su har da baki yan kasashen Birtaniya da Holland da Amurka.

Wani bangaren da harin ya faru a kasar Sri Lanka
Wani bangaren da harin ya faru a kasar Sri Lanka LAKRUWAN WANNIARACHCHI / AFP
Talla

Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya, Fafaroma Francis da ya jagoranci addu’ar Easter, ya bayyana takaicin sa da harin, inda ya yi addu’a ga mamatan da kuma fatar Allah zai sa 'yan ta’addan su tuba.

Firaministar Birtaniya, Theresa May wadda ita ma ta yi tir da harin, ta bukacin hadin kan duniya wajen ganin kowa ya gudanar da addinin sa ba tare da fargaba ba.

Shugaba Donald Trump ya aike da sakon jaje da kuma fatar alherin Amurkawa ga mutanen Sri Lanka kan abinda ya kira kazamin hari kan mujami’u da otel, inda yace a shirye suke su taimakawa kasar.

Firaministan Holland Mark Rutte ya mika sakon jaje ga iyalan wadanda harin ya ritsa da su, yayin da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ke cewa, babu yadda kyama da zub da jini zai samu nasara.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana fatar ganin an hukunta wadanda suka kitsa harin, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana goyan baya ga mutanen Sri Lanka da gwamnatin kasar.

Sauran wadanda suka aike da sakon jaje sun hada da Firaministan Israila Benjamin Netanyahu da takwaran sa an India, Narendra Modi da shugaban kungiyar kasashen Turai, Jean-Claude Juncker.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.