Isa ga babban shafi
Sri Lanka

IS ta dauki alhakin harin Sri Lanka

Kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamar da hare-haren kunar-bakin wake da suka kashe sama da mutane 320 a Majami’u da Otel Otel a Sri Lanka. Tuni jami’an ‘Yan Sanda suka cafke mutane 40 da ake zargi da hannu a harin, yayinda al’ummar kasar suka fara zaman makoki a yau Talata.

An tabbatar da mutuwar sama da mutane 320 a harin Sri Lanka
An tabbatar da mutuwar sama da mutane 320 a harin Sri Lanka 路透社
Talla

Kungiyar IS ta dauki alhakin ne bayan sa’o’i 48 da kai kazaman hare-haren da suka rutsa da baki ‘yan kasashen waje a daidai lokacin gudanar da bukukuwan Easter a karshen makon da ya gabata.

Sanarwar da IS ta fitar na zuwa ne, bayan gwamnatin Sri Lanka ta ce, bincikenta na farko ya nuna cewa, an kai hare-haren ne a matsayin ramakon farmakin da wani dan bindiga ya kai a New Zealand, in da ya kashe mutane 50 a wasu Masallatai biyu na Chritschurch.

Da farko dai, gwamnatin Sri Lanka ta zargi wata karamar Kungiya mai suna National Thawheeth Jamna’ath da kai hare-haren, amma ta ce, tana kan gudanar da bincike kan ko wannan kungiya na samun goyon baya daga ketare.

A yayin ganawa da manema labarai, Firaministan kasar Ranil Wickremesinghe ya ce, “Ga alama akwai hannun wasu daga kasashen ketare a wannan harin, ana ganin wasu daga cikin maharan sun yi tafiya zuwa kasar waje, sannan suka dawo cikin wannan kasa, akwai yiwuwar adadinsu ya zarce wanda ake tunani, amma za mu gudanar da bincike. Muna kuma son kasashen duniya suma su gudanar da nasu binciken saboda akwai ‘yan kasashensu da aka kashe a wannan harin”.

Tuni al’ummar kasar ta Sri Lanka suka fara zaman makoki a yau Talata, in da jama’a suka yi tsit na mintina uku, yayinda kuma aka fara jana’izar mutanen da suka rasa rayukansu a harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.