Isa ga babban shafi
Sri Lanka

Sri Lanka za ta yi wa sojinta garambawul bayan harin kasar

Shugaban Sri Lanka, Maithripala Sirisena ya sha alwashin yin garambawul tsakanin masu rike da manyan mukaman sojin kasar, biyo bayan hare- haren kunar bakin wake da aka kaddamar kan Majami'u da Otel Otel na kasar, abinda ya lakume rayuka sama da 359.

Wasu daga cikin sojojin Sri Lanka
Wasu daga cikin sojojin Sri Lanka REUTERS/Dinuka Liyanawatte
Talla

Shugaba Sirisena, wanda shi ne Ministan Tsaro ya ce, zai sake fasalin hukumomin tsaron kasar da ‘yan sandan da ke karkashinsa.

A wani jawabin da ya gabatar ga al’ummar kasar, shugaba Sirisena ya ce, yana fatan gudanar da sauye-sauyen tsakanin sojin cikin sa’o’i 24, yayinda cikin mako guda zai kammala sake fasalta rundunar 'yan sandan kasar.

Firaministan kasar, Ranil Wickremesinghe, ya tabbatar da cewa ‘yan sanda sun samu bayanan sirri kafin hare-haren kunar bakin waken na ranar Lahadin da ta gabata.

Firaministan ya shaida wa manema labarai jim kadan kafin jawabin shugaban kasar cewa, ana daf da kaddamar da bincike kan dalilin da ya sa ‘yan sanda ba su sanar da ofishinsa game da bayanan sirrin ba.

Tuni kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamar da hare-haren, in da ta wallafa hotunan mayakanta da ta ce, sune suka kai farmakin na kunar-bakin wake.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.