Isa ga babban shafi
Sauyin Yanayi

Wasu halittu na gab da bacewa daga doran-kasa

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, kusan nau’ukun halittu miliyan guda ne ke fuskantar barazanar bacewa daga doran-kasa sakamakon tasirin sakacin bil’adama.

Sauyin yanayi na barazana ga bacewar wasu nau'ukan halittu miliyan guda daga doran-kasa
Sauyin yanayi na barazana ga bacewar wasu nau'ukan halittu miliyan guda daga doran-kasa AFP/Prakash MATHEMA
Talla

Daftarin Kudurin Majalisar Dinkin Duniya da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya samu kwafinsa, ya bayyana gurbacewar iska da rashin tsaftataccen ruwan sha da kuma yadda turiri ke gurbata gandayen daji har ma da rashin auratayya tsakanin tsirrai da rashin kifaye masu gina jiki da rashin itatuwan gumbi ko kuma Mangroves a Turance da ke tare guguwa, a matsayin kadan daga cikin abubuwan da ke haifar da barazanar sauyin yanayi.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa, akwai alaka tsakanin dumamar yanayi da kuma bacewar wasu nau’ukan halittun duniya.

Ana saran wakilan kasashen duniya 130 da za su gana a birnin Paris a ranar 29 ga wannan wata na Afrilu, su yi nazari mai zurfi kan wannan rahoto, in da ake saran a sauya wasu kalmomin da ke kunshe a cikinsa, ba tare da sauya alkaluman da aka bayyana a cikinsa ba.

Shugaban kwamitin da ya tattara rahoton na Majalisar Dinkin Duniya, Robert Watson, ya ce, sun fahimci cewa, batun dumamar yanayi da bacewar wasu na’ukan halittu na da muhimmanci sosai ba wai ta fuskatar kare muhalli ba, hatta ta bangaren ci gaba da kuma bunkasa tattalin arziki.

Jami’in ya ce, yadda muke dafa abincinmu da kuma fitar hayaki na zagon-kasa ga kariyar da muke samu daga halittu daban daban, yayinda ya ce, sauya hali ne kawai zai hana gamuwa da illa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.